Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake juyayin kwashe dalibai 42 a kwalejin kimiyya ta garin Kagara, wanda ‘yan bindiga suka yi. Lamarin da ke kara nuna tabarbarewar tsaron da ya sa ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a jihar Neja.
A cewar wani babban Jami’in karamar hukumar Sarkin Pawa, wanda ya nemi a boye sunansa saboda dalilai na tsaro, ‘yan banga hudu ne aka kashe wadanda ke taimaka wa jami’an tsaro a yankin, tare da kwashe wasu mutum 10.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin jihar Neja da rundunar ‘yan sandan jihar ba su ce komai ba akan wannan hari da aka kai Sarkin Pawa.
Amma alokacin da yake karbar wasu ‘yan sandan kwantar da tarzoma 300, kwamishinan yan sandan jihar Neja, Adamu Usman, ya ce jami’an tsaro sun kara daura damara domin tunkarar maharan don kubutar da yan makarantar Kagara.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Karin bayani akan: Sarkin Pawa, Nigeria, da Najeriya.