Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi ya ce idan har tattaunawa da masu ruwa da tsaki zai kawo karshen wannan tashin hankali to suna maraba da yin haka.
Ya yi wannan bayanin ne a lokacin da tawagar gwamnonin ta ziyarci jihar Neja domin alhenin sace fasinjan bas da aka sako da kuma daliban kwalejin kimiyya ta garin Kagara.
Ya kara da cewa idan har wanna ita ce hanyar da za a samu zaman lafiya to za su bi haka, kuma idan ta kama ko wane irin abu ne za su yi shi don kawo karshen wannan tashin hankali da ake ciki a yanzu.
Shi ma gwamnan jihar Nejan, Alhaji Abubakar Sani Bello ya yi kira ga gwamnonin da su hada hannu don kawo karshen wannan matsala ta rashin tsaro. Ya kara da cewa "lokaci yayi da ya kamata mu mike tsaye, mu tabbatar cewa Gwamnatin tarayya ta yi abinda ya kamata don ba mu muke iko da rundunar sojoji da na ‘yan sanda ba."
A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: