Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10 A Jihar Nejan Najeriya, Sun Yi Awon Gaba Da Wasu


Daruruwan mutane sun tsere daga garin Shadadi a yankin karamar hukumar Mariga dake cikin jihar Nejan Najeriya bayan da 'yan bindiga suka aukawa garin.

Mazauna garin sun ce maharan sun yi ta bin gida-gida da rana tsaka suna cin zarafin mutane inda daga karshe suka kashe mutum 10 tare da yin awon da gomman mutane kamar yadda wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatarwa da VOA.

Shaidu sun ce maharan sun shiga garin tun wajen karfe bakwai na safiya kuma suka yi akalla awa takwas a gidajen mutane suna kwace kudi da wasu dukiya.

Mutumin da ya ce a sakaya sunansa ya kara da cewa bayan maharan sun yi ta harbe-harbe a cikin garin, sun karbe wa wani mutum miliyan uku, sun kashe mutum goma.

Haka zalika ‘yan bindigar sun auka garin Kuimo duk a karamar hukumar ta Mariga suka kona karamin ofishin ‘yan sanda tare da kashe mutun daya kamar yadda wani da ya tsallake rijiya da baya ya fadawa VOA.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai kokarin jin ta bakin ‘yan sandan jihar Nejan akan wannan al’amari ya ci tura, to amma gwamnatin jihar Nejan ta ce ta hada hannu da jamin’an tsaro domin shawo kan wannan ta’addanci in ji Gwamnan jihar Nejan Alhaji Abubakar Sani Bello.

Saurari rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum10 A Jihar Nejan Najeriya, Sun Yi Awon Gaba Da Wasu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00


TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG