Hukumomi dai sun ce Amina Aliyu tana hannunsu, kuma tana amsa tambayoyi kan kisan kishiyarta mai suna Fatima Ibrahim yar kimanin shekaru 17. ta hanyar rabka mata itace da kuma yunkurin konata ta hanyar banka ma dakinta wuta.
A hirar shi da Muryar Amurka, Alhaji Aliyu Abdullahi, mijin matan guda 2 wadda aka kashen dake zaman Amarya da Uwar gida da ake zargin ta yi kisan yace yana cikin wani yanayi na tashin hankali.
Karin bayani akan: Amina Aliyu, Minna, Fatima, Nigeria, da Najeriya.
Alhaji Abdullahi ya bayyana cewa, bai taba tunanin wannan lamarin zai iya faruwa a gaidansa ba. Bisa ga cewarshi, uwargidansa ta kashe kishiyartan ne tare da taimakon kanwarta wadda suka hadu suka buge ta da tabarya kuma bayan ta mutu su ka yi kokarin cinnawa dakinta wuta. Ya kuma yi kira ga hukumomi da jami’an ‘yan sanda su ci gaba da gudanar da bincike a kan wannan lamarin.
A na shi bayanin, Malam Ibrahim Yahaya Sidi, mahaifin marigayiya Fatima yace yana fatan hukumomin za su bi masa hakkin diyarsa da aka kashe.
Gwamnatin jihar Nejan dai tace tasamu wannan Labari kuma za ta yi duk abinda ya wajaba domin tabbatar da an hukunta mai laifi inji daraktar kula da ma'aikatar kare hakkin mata da yara a jihar Barista Maryam Kolo. Ta ce hukumomi za su tabbatar an gudanar da cikakken bincike an kuma yanke hukumci yadda ya kamata.
Shi ma a nasa bayanin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Nejan Adamu Usman yace a yanzu suna rike da Mutane 4 akan wannan al’amari .
Tuni dai aka kai gawar Fatima gidan mahaifinta dake jihar Katsina kuma aka gudanar da jana’izarta da yammacin Laraban nan.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari cikin sauti: