Bayanai dai sun nuna cewa rikicin ya barke ne bayan da aka hana wasu dalibai mata musulmi shiga makarantar sakandaren Baptist da ke birnin Ilorin.
Dama dai wannan sakandare ta Baptist ta na daya daga cikin makarantu 10 da tun farko gwamnatin jihar Kwara ta rufe a lokacin da ta bayar da damar cewa masu sha'awa suna iya sanya hijabin.
Dr. Idowu Ibitoye, shi ne sakataren kungiyar kiristoci ta CAN reshen jihar Kwara,ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta mutunta doka tunda wannan batu na sanya hijabi ya na gaban kotun kolin Nigeria, sannan ya yi kira ga mabiya bangarorin addinan biyu, wato musulmi da kirista da su kai zuciya nesa domin dorewar zaman lafiya.
Karin bayani akan: Shugabannin Addinai, Okasammi Ajayi, jihar Kwara, CAN, Nigeria, da Najeriya.
Shi ma shugaban kungiyar musulunci ta Izala a jihar Kwara Sheikh Mas'udu Offa, ya ce bai kamata wannan al'amari ya tayar da hankali ba tunda dama mutanen jihar Kwara dukkaninsu 'yan uwan juna ne.
Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa akan lamarin, sakataren yada labaran gwamnan jihar Kwara Rafi'u Ajakaye, ya ce ba zai yi magana a madadin gwamnati ba game da batun, sai dai a jira sanarwar gwamnati.
Rundunar 'yan sandan jihar Kwara ta ce ta dauki mataki domin tabbatar da maido da cikakken zaman lafaiya a birnin na Ilori, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga kakakin 'yan sandan jihar SP Okasammi Ajayi ta nuna.
Saurari rahoton Mustapha Nasiru Daga Minna.