Jihar Nejan Nigeria ta sanar da rufe illahirin makarantun sakandaren jihar har na tsawon makonni biyu daga yau dinnan Jumma'a a matsayin kandagarki da kuma samun lokacin kara nazarin al'amarin tsaro da makomar dalibai.
A wata Sanarwa daga Ofishin Kwamishiniyar Ilimi ta jihar Nejan, Hajiya Hannatu Jibrin Salihu, gwamnatin ta ce sun rufe makarantun ne saboda dalilai na tsaro bayan wani taro da masu ruwa da tsaki akan sha'anin ilimin da shugabannin tsaro a jihar Nejan.
Dr.Isa Adamu, shugaban Hukumar Bada Ilimi Bai Daya a jihar Nejan, yayi karin haske akan wannan mataki na rufe Makarantun, musamman ganin yadda ake bukatar natsuwa kafin a iya koyar da daliban har kuma su gane.
To amma masana harkokin ilimi a jihar na gani akwai sake game da matakin rufe makarantun kamar yadda daya daga cikinsu, Aliyu zakariyya kontagora, wanda aka fi sani da Canza-Shi-Malam ya yi takaicin illar hakan ga batun samar da ilimi wanda ake matukar bukata.
Tun bayan kwashe Daliban Kwalejin kimiyya a garin Kagara ne dai gwamnatin jihar Nejar ke kara matsa kaimi a yaki da yan bindiga da suka addabi jama'a a jihar Nejar dama wasu jihohi na arewacin Nigeria.
Ga Mustapha Batsari da cikakken rahoton: