A yayinda bukukuwan salla ke gabatawo, hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya da ake kira FRSC a takaice ta tura jami'ai 35,000 don kula da manyan hanyoyin kasar mussamman a lokacin bikin sallah da za a yi ranar Talata mai zuwa.
Yanzu haka al’ummomin da suka koma yankunansu da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya na kokawa game da batun rashin sabunta katunan zabensu.
Komi ya tsaya cik a kasar Zimbabwe yayinda ake jiran hukumcin kotu akan zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan da ya gabata, wanda shine karon farko ba tare da tsohon shugaba Robert Mugabe ba.
Mayakan Taliban sun kwace wani sansanin sojoji a arewacin Afghanistan sun kuma kashe sojoji dayawa tareda yin awon gaba da wasu.
‘Yan sanda a birnin London sun ce wani mutum ya afka cikin wani gungun masu tafiya da kafa da mota kafin ya banke wasu shingaye dake wajen ginin majalisar dokokin Burtaniyya yau Talata, wasu mutane sun jikkata sakamakon hakan.
Manoma Tumatir a Najeriya sun ce hukumar kwastam da takwararta ta NAFDAC mai kula da harkokin ingancin abinci da magunguna ta kasa, sun sa sun yi asarar kimanin Naira Miliyan dubu goma a kakar noman tumatir ta bana.
A Najeriya masu fashin bakin al’amurran yau da kullum sun suna ci gaba da bada fassarar da bamdabam dangane da batun toshe kofar shiga majalisar dattawa da jami’an tsaro su kayi, wanda ya janyo korar babban darektan hukumar tsaron farin kaya na kasar Lawal Daura.
A karshen makon jiya ne hukumar UNDP tare da hadin gwiwa da gwamnatin kasar Japan suka kaddamar da shirin bada kayan noma kyauta ga mazauna kauyen Loko, na karamar hukumar Song a jihar Adamawa.
Cikin fursunoni 800 da aka yiwa afuwa har da matar tsohon shugaban Ivory Coast Simone Gbagbo.
Ma'aikatar kiyaye gobara ta jihar California ta ce ta yiwu a iya shawo kan gobarar dajin a cikin mako mai zuwa.
Fadar ta shugaban Najeriya ta nesanta Shugaba Buhari da alhakin tura kudurin doka na rage ‘yancin yada labarai wanda ya sami karatu na biyu a gaban majalisar dattawan kasar.
Yanzu haka wannan tafiyar ta janyo cece-ku-ce tsakanin ‘yan siyasar kasar dake zargin cewa batun lafiya ne zai kai shugaba Buhari Ingila.
A cikin ‘yan kwanakin nan rahotanni na nuna cewa mayakan kungiyar Boko Haram suna sauya salon kai hare-harensu ciki har da kisan dauki daidai, da kuma na sari-ka-noke, da kona kauyuka ko kuma dasa bama bamai a gonaki.
Wasu jihohi 8, da birnin Washington a gundumar Columbia sun kai karar gwamnatin shugaba Donald Trump akan ba wani dan jihar Texas damar raba ka’idodin yadda za a yi wata irin bindiga mai amfani da na’urar 3D.
Shugaba Trump ya ce yana iya dakatar da ayyukan kasarsa idan bai sami amincewar gina ganuwa tsakanin Mexico kasar sa ba.
Jiya litinin Shugaban Amurka Donald Trump yayi wani cikakken bayani da bai taba yi ba a baya cewa, a shirye yake yayi ganawar kai-tsaye da Iran.
Yanzu haka ‘yan kasar Zimbabwe na dakon sakamakon muhimmin zaben da aka yi a kasar, wanda wasu dayawa ke fatan ta yiwu, ya kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar da ke fuskantar koma baya bayan mulkin tsohon shugaban kasa Robert Mugabe mai tsauri da yayi na tsawon shekaru 38.
A Jamhuriyar Nijer, jarabawar ajin karshe a makarantun share fagen shiga jami’a da aka gudanar a tsakiyar watan nan na Yuli ta bar baya da kura bayan da wata cibiyar jarabawa ta bayyana sunan wani dalibin da ya rasu a jerin wadanda suka yi nasara.
Domin Kari