An kai hare-haren rokoki a birnin Kabul da safiyar yau Talata, a lokacin da shugaba Ashraf Ghani ke jawabin bikin babbar sallah a wata liyafa ta musamman da aka shirya a fadarsa. Akalla roka daya ta dira kusa da fadar shugaban kasar.
‘Yan sanda sun ce wasu ‘yan kunar bakin wake su 5 sun boye a bayan masallacin Eidgah inda suka harba rokoki da yawa daga can zuwa sassan garin dabam dabam. Wata majiyar jami’an tsaro ta tabbatar da cewa mayakan sun harba akalla rokoki 10 amma kafafen yada labaran yankin sun ce adadin ya zarta haka.
4 daga cikin maharan sun mutu a arangamar da suka yi da jami’an tsaron yankin. Akalla dan sanda daya ya jikkata. Kafar yada labaran Tolo a Afghanistan ta fadi cewa an ga wani jirgin sama mai saukar Ungulu yana shawagi a yayinda yake auna maharan a wuraren da suka boye kusa da masallacin na Eidgah.
Shugaba Ghani, wanda ya cigaba da jawabinsa a wajen liyafar, ya ce wadannan hare-haren ba zasu firgita Afghanistan ba. Ya kuma ce dama gwamnati ta shirya don aukuwar irin wannan lamarin a ranar sallah.
Facebook Forum