Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya Yiwa Fursunoni 800 Afuwa


Cikin fursunoni 800 da aka yiwa afuwa har da matar tsohon shugaban Ivory Coast Simone Gbagbo.

Uwar gidan tsohon shugaban Ivory Coast Simone Gbagbo na daya daga cikin firsinoni 800 da shugaba Alassane Ouattara ya yiwa afuwa jiya litinin, firsunonin dai an garkame su ne akan laifuffukan da suka danganci mummunan yakin basasar da aka yi a kasar a shekarar 2011.

An yankewa Simone Gbagbo hukuncin zuwa gidan yari na tsawon shekaru 20 a shekarar 2015 bayan da aka tabbatar da cewa ta taka rawa a tashin hankalin da ya jefa yanayin tsaron kasar cikin halin kaka-na-kayi. A shekarar da ta gabata kuma an gurfanar da ita gaban kotu amma aka wanke ta daga zarge-zargen keta hakkin bil’adama da aka yi mata.

Masu gabatar da kara sun zargi Simone da jagorantar gungun wasu bata gari wajen kaiwa abokan hamayyar mai gidanta, tsohon shugaba Laurent Gbagbo harin ramuwar gayya, ciki har da sama masu makamai da jiragen sama masu saukar ungula na kai hari.

Kimanin mutane 3,000 suka mutu a kasar dake yammacin Afrika a shekarar 2011 bayan da Laurent Gbagbo ya ki ya amince da kayen da ya sha a Ouattara a zaben da aka yi cikin watan Nuwambar shekarar 2010. Daga baya an kama Gbagbo aka kuma mika shi ga kotun duniya dake birnin Hague, inda ake tuhumarsa akan laifuffukan keta hakkin bil’adama.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG