A cewar wata sanarwa da kakain fadar shugaban, Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi ne zai rike ragamar mulkin kasar har zuwa lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya dawo.
Wasu 'yan kasar na gani batun kiwon lafiya ne zai kai shugaba Buhari Ingila ba hutu kadai ba.
Wakilin sashen Hausa Umar Faruk Musa, ya tattauna da Malam Garba Shehu akan wannan batun inda ya ce, wannan ba abin mamaki bane, don ko a shekarar da ta gabata wasu cewa suka yi shugaba Buhari ya mutu a Ingila. Ya kuma ce, ai shugaba Buhari bai fi karfin yin rashin lafiya ba kuma bisa ka’idar aiki shugaban kasa na da kwanakin hutu 30 a duk shekara yana kuma da damar ya rarraba yadda zai dauki hutunsa.
Sai dai wannan hutun na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da kwamacalar siyasa a Najeriya, abinda wasu ke gani ya kamata a ce shugaban ya daidaita rigingimun dake faruwa. Malam Garba Shehu ya ce, hayaniyar siyasar dake faruwa a kasar ba ta tadawa shugaba Buhari hankali kuma ba ta hana shi gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
“Babu wasu sharudda da aka gindayawa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo akan yadda zai tafiyar da harkokin mulkin kasar baya ga wadanda kundin tsarin mulki Najeriya ya tanada.” a cewar Garba Shehu.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum