Hukumomi a jihar California dake yammacin Amurka sun ce gobarar dajin ta fara ci sama da mako daya ta zama mafi muni a tarihin gobarar dajin da aka taba gani a jihar.
Gobarar, da aka sanyawa sunan Mendocino Complex, ta kasu kashi biyu a wani bangaren arewacin jihar, daga nan ta zo ta hade ta kuma kona hecta 115,000 abinda ya zarta barnar da gobarar Thomas da ta faru a watan Disambar shekarar 2017.
Ma’aikatar kiyaye gobara da kula da gandun daji ta jihar California ta ce ya zuwa daren jiya litinin kashi 30 ne kadai aka iya magancewa na gobarar kuma ta cigaba da karuwa. Haka kuma ya zuwa yanzu gobarar ta lalata gidaje 150.
Kusan jami’ai 4,000 ne ke aikin kashe gobarar, ciki har da ma’aikatan dake tuka jiragen sama masu saukar unglu da wasu jiragen na sama dake yin feshi daga sama.
Facebook Forum