Sama da gidaje 200 ne suka lalace sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a karamar hukumar Maru dake jihar Zamfara.
Manoman shinkafa a jihohin Kano, Jigawa da Katsina sun koka game da tsarin bada lamunin kayan noma karkashin shirin gwamnatin tarayya na tallafawa masu noman karkashin kulawar babban bankin kasar.
Direbobin tasi guda 11 sun mutu, wasu su su 4 kuma sun sami munanan raunuka a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka budewa motarsu wuta a Afrika ta kudu.
Sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce gwamnatin Iran ta zama alakakai ga al’ummar ta, ya kara da cewa Amurka bata tsoron ta kaiwa gwamnatin kasar farmaki a matakin koli yayinda Amurka din ke yin kira ga dukan abokan kawancenta su hada hannu wajen murkushe gwamnatin.
Bakin haure 318 da suka fito daga kasashe dabam dabam na yammacin Nahiyar Afrika, kasar Algeria ta taso keyarsu zuwa iyakar ta da Janhuriyar Nijar.
Manyan jami’an Amurka da na Afghanistan da yawa sun tabbatar da wannan matakin, a cewar jaridar.
Bude ofishin jakadancin shine ya kawo karshen ziyarar kwanaki uku da Isaias Afwerki, shugaban Eritrea ya kai Habasha.
Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu wanda ke ziyarar aiki a kasashen turai yace kasar Iran na iya haddasa kara kwararar 'yan gudun hijira a kasashen Turai idan ba a dauki mataki ba
Tsohon mai bincike na musamman Robert Mueller ya zargi Manafort da yin magana da wasu shaidu akan binciken da ake yi mashi.
Jiragen saman yakin Isra’ila sun kai hare-hare yau Talata a zirin Gaza, inda suka auna wuraren ‘yan kungiyar mayaka masu zafin kishin addinin Islama.
Ana zargin dakarun tsaron Afghanistan na musamman, da dakarun Amurka ke marawa baya da kisan fararen hula guda 9 da kuma raunana wasu su 8 a gabashin lardin Nangarhar, wadanda ga dukan alamu anyi zaton mayakan ISIS ne.
Rayuka da dama sun salwanta a shekarun baya sakamakon bullar cutar Ebola, amma maganin rikafin cutar da aka samo yanzu zai taimaka matuka wajen dakile cutar.
Wani jami'in lardin Ghazni ya fada yau Talata cewa, 'yan kungiyar Taliban sun iya kwace gundumomi biyu, Jaghatu da Dehak, bayan wani mummunan fada a daren jiya.
Amurka ga gargadi Iran ta sauya dabi'unta idan ba haka ba zata dauki matakan matsin lamba kan kasar. Sai dai ba a fayyace iya matsin lambar da Amurka zata iya yi, ba tare da kasashen Turai ba, dake aiki da Iran don ceto yarjejeniyar Nukiliyar.
Jami’an koriya ta kudu sun fada ranar Lahadi cewa Kim ya shirya zai gayyaci kwararru, da ‘yan jarida daga koriya ta kudu da Amurka don su kasance wurin a lokacin da za a rufe cibiyar.
Domin Kari