A yayinda zabukan ‘yan majalisar dokokin Amurka na rabin wa’adi da za a yi a watan Nuwamba ke cigaba da karatowa, ‘yan jam’iyyar Republican na sa ido akan farin jinin shugaba Donald Trump, wanda a yanzu yake kusan kashi 42 cikin dari.
Kwarjinin Shugaba Trump ya cigaba da kasancewa kasa da kashi 40 cikin dari, bisa wasu sabbin binciken ra'ayoyin jama’a guda biyu da aka gudanar. Binciken ra'ayoyin jama'a da kamfanin Gallup ke gudanarwa mako-mako ya nuna cewa, kashi 42 cikin dari na Amurkawa suka gamsu da salon shugabancin sa yayinda kashi 52 kuma basu gamsu ba.
Wani sabon bincike kuma daga jami’ar Monmouth ya gano cewa kashi 43 na Amurkawa sun gamsu da salon mulkin Trump, yayinda kashi 50 cikin dari kuma basu jin dadin salon mulkin sa.
Bisa tarihi, jam’iyyar shugaban kasa ta kan yi asarar kujeru da yawa a zabukan rabin wa'adi idan farin jinin shugaban yayi kasa da kashi 50 cikin dari. Tsofaffin shugabannin Amurka Bill Clinton da Barack Obama dukansu sun rasa kujeru fiye da 50 a majalisar dokokin kasar a zabukan rabin wa'adi na farko da aka gudanar bayan hawansu mulki, kuma farin jininsu a wancan lokacin ya dan dara na Trump a yanzu.
Facebook Forum