Majalisar Koli ta Musulunci a Najeriya (NSCIA), karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bukaci Musulmi a fadin kasar da su fara duban jinjirin watan Ramadan na 2025 (1446 AH) daga ranar Juma’a.
Abubakar ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da Sakatare-Janar na NSCIA, Farfesa Is-haq Oloyede, ya sanyawa hannu a ranar Alhamis.
“Sakamakon shawarar da Kwamitin Duban Wata na Kasa (NMSC) ya bayar, Shugaban Majalisa yana kira ga al’ummar Musulmi a Najeriya da su fara duban jinjirin watan Ramadan 1446 AH da zarar rana ta fadi a ranar Juma’a, 28 ga Fabrairu, 2025, wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban, 1446 AH.”
Majalisar ta yi addu’a cewa Allah ya ba wa kowane Musulmi rai da lafiya don halartar ibadar Ramadan tare da cin gajiyar albarkar da ke cikin watan.
Majalisar ta kuma bayyana cewa, baya ga shugabannin addini na yankuna da aka saba tuntuba a kowace unguwa, za a iya tuntubar wasu mambobin Kwamitin Duban Wata na Kasa (NMSC) domin tabbatar da sahihin bayani kan ganin jinjirin watan Ramadan 1446 AH.
Dandalin Mu Tattauna