Yanzu dai kimanin makonni biyu kenan babu hasken wutar lantarki a daukacin yankin na arewacin Najeriya birni da karkara.
Zaben kananan hukumomi da aka yi a ranar sabar a jihar Kano ya gamu da kalubalen rashin fitowar jama’a rumfunan zabe.
Zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Kano yau asabar, 26 ga watan Oktoba na 2024, ya gamu da kalubalen rashin fitowar Jama’a domin kada kuri’a kuma Jami’an tsaro musamman ‘yan sanda su ma basu fito aikin bada tsaro ba.
A cewar Gezawa ba za su bayyana sunaye ko jam’iyyun da ‘yan takarar suka fito ba yana mai cewa hurumi ne na jam’iyyun su bayyanawa jama’a idan suna so.
Gwamnan ya ce majalisar tsaro ta jihar Kano ta amince da wannan mataki kuma dokar ta fara aiki nan take.
Hukuncin kotun na yau Alhamis ya rushe ko soke sanya hannu akan dokar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a ranar da majalisar ta kammala aikinta akan daftarin dokar
Babbar kotun tarayya dake Kano ta ce ta gamsu da hujjojin ta masu kara suka gabatar, saboda haka tana da hurumin sauraron shari'ar takaddamar sarautar Kano.
Da misalin karfe 12 na ran nan ne alkalin kotun mai sharia M.A Liman ya zauna domin sauraron shari'ar.
Yanayi ya fara dumama a birnin Kano da kewaye sakamakon saukar mai martaba sarkin Kano da gwamnati ta cire Alhaji Aminu Ado Bayero a filin sauka da tashin jiragen sama na Kano.
A shekara ta 2022 ne shugaban bankin raya musulinci wato IDB, Dr Muhammad Al-Jasser ya kaddamar da shirin bankin na raya noma da kiwo a jihar Kano da nufin samar da abinci da dakile rikici tsakanin manoma da makiyaya
Kwana biyu bayan kaddamar da katin lamuni na kudin dala a Najeriya, wato American Express Credit Card, irinsa na farko a Afrika, masana tattalin arziki sun fayyace bambancinsa da kudin Crypto, yayin da masu masana’antu ke cewa, akwai bukatar wayar da kan ‘yan kasuwa akan alfanun aiki da katin.
Babbar kotun Kano karkashin jagorancin mai shari’a Usman Na’Abba ta bada odar dake tabbatar da dakatarwar da wasu shugabannin Jam’iyyar APC na mazabar Ganduje a karamar hukumar Dawakin Tofa su ka yi a shekaranjiya litinin.
Cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, wadda sakataren gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim ya sanyawa hannu, gwamman jihar Umar Namadi, ya bada umarnin dakatar da kwamishinan ciniki da masana’antu Alhaji Aminu Kanta, bisa zargin sa da hannu a almundahana.
Domin Kari