Kungiyar Kiristan Najeriya, CAN, reshen Jihar Kaduna ta ce duk da ikirarin nasara kan 'yan-bindiga da gwamnati ta yi, har yanzu akwai matsalar tsaro a wasu yankunan Jihar Kaduna saboda ko a Larabar da ta gabata 'yan-bindigan sun sace wasu mutane 57 a wani yanki na karamar hukumar Kajuru.