Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KADUNA: Pastor Ya Tallafawa Makarantar Allo


Makarantar Allo
Makarantar Allo

A yayin da ake cigaba da bukin ranar zaman lafiya ta duniya a yau Laraba, Shugaban Kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya, Pastor Yohanna Buru ya kai tallafin kayan karatu a wasu makarantun Allo na jahar Kaduna don kyautata alaka tsakanin Musulmi da Kirista.

Ranar 21 ga watan Satumbar kowacce shekara dai ita ce ranar zaman lafiya ta duniya kuma a jahar Kaduna, malaman addinin Kirista da Musulmi sun yi amfani da ranar wajen raba kyaututtukan kayan karatun allo a wasu makarantu.

Makarantar Allo
Makarantar Allo

Malam Lawal Muduru na cikin 'yan-tawagar Pastor Yohanna Buru kuma ya ce aikin da kungiyar wanzar da zaman lafiyan ke yi na kara kyautata alaka tsakanin Kirista da Musulmi.

Daya daga cikin Malam makarantun allon da aka kaiwa allunan rubutu da dawada, ya ce lallai zumunci ya kullu.

A baya can dai jahar Kaduna na cikin Jihohin da aka yi ta samun rikicin Kabilanci da addini, sai dai ire-iren wadannan tarurruka sun kara wayar da kan al'uma da sauran mabiya ta yadda yanzu ake zaune lafiya da juna.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG