Ganin yadda Malamai kan ba da mabanbantan fatawoyi kan aikin hajji, ya sa hukumar kula da aikin hajji da zuwa Jerusalem ta Jihar Kaduna fitar da sabbin tsare-tsaren aikin hajji ga maniyyata a wannan shekara ta 2023.
Sa'o'i kadan da tabbatar da kashe jami'an hukumar tsaro ta farin kaya bakwai a yankin Birnin Gwari, shugabannin al'uma a yankin sun ce akwai sauran rina a kaba idan gwamnati ba ta dauki sabbin matakai ba.
Shirin sayar da gidajen ma'aikata a kwalejin kimiya da fasaha da ke Kaduna, ya raba kawunan kungiyoyin ma'aikatan kwalejin, domin a yayin da kungiyar malaman kwalejin ta ce ba ta yadda a saida gidajen ba, ita kungiyar manyan ma'aikata cewa ta ke ta na goyon bayan matakin dari-bisa-dari.
A cigaba da samun 'yan Najeriya masu kokarin ganin an zauna lafiya tsakanin al'ummomi daban daban, wata Musulma ta agaza wa mata Kirista mabukata.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kaddamar da taron yakin neman zaben ta na Arewa maso yammacin Najeriya.
Ganin yadda aka fara samun matsaloli a wasu wuraren yakin neman zaben jam'iyyu ya sanya hukumar wanzar da zaman lafiya ta jahar Kaduna da hadin gwiwar wasu kungiyoyi, kiran taron masu ruwa da tsaki don gudanar da yakin neman zabe, da kuma zabubbuka lafiya a fadin jahar.
Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya sun ce matsalar tsaro da talauci su ne manyan matsalolin da su ke sa ake aurar da yara da wuri da kuma cin zarafin yara mata a yankin.
Ganin yadda ake yawan samun rahotannin aikata fyade a wasu sassan Jihohin Arewacin Najeriya ya sa gwamnatin jihar Kaduna fito da wani tsarin jadawalin masu aikata fyade don fallasa su a duk inda su ka shiga da nufin kawo karshen wannan ta'annati a tsakanin al'umma
An sake arangama tsakanin 'ya'yan kungiyar Ansaru da kuma 'yan-bindiga a yankin Damarin karamar hukumar Birnin Gwari sakamakon da aka kashe 'yan bindiga biyar.
A yayin da majalissar dinkin duniya ta ware ranakun 13 zuwa 16 a matsayin makon fahimtar juna tsakanin mabanbanta addinai da kabilu, malaman addinin Kirista a jahar Kaduna sun karrama wani matashi da ya haddace al-qur'ani.
MANUNIYA: Matsayin Shugabannin Fulanin Najeriya Game Da Zaben 2023, Nuwamba 11, 2022
Domin Kari