Hukumar tsaro ta farin kaya da aka fi sani da Civil Defence ce dai ta fitar da sanarwar tabbatar da kashe jami'an ta guda bakwai da kuma wasu jami'an tsaro biyar da aka ce sojoji ne, a wani wurin hakar ma'adanai dake yankin Kuriga a karamar hukumar Birnin Gwari sakamakon kwanton baunar da 'yan bindiga su ka yi musu.
Jim kadan bayan fitar da wannan sanarwa ne sai Dan-masanin Birnin Gwari, Alh. Zubairu Idris Abdurra'uf ya jawo hankalin gwamnati cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa game da abubuwan da ke faruwa a yankin na Birnin Gwari.
Abdurra'uf ya ce rufe wuraren hakar ma'adanai da ke Manini kusa da Kuriga kawai shine maganin matsalolin hare-haren 'yan bindiga a yankin. Kuma ya ce akwai bukatar kara jami'an tsaro da makamai a yankin Birnin Gwarin baki daya.
Masani kan harkokin tsaro, Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce akwai abubuwan da ya kamata jami'an tsaro su kiyaye game da wuraren da ake hakar ma'adanai.
Manjo Shinko ya ce dama 'yan bindiga sun fi zama wuraren da ke da arzikin kasa irin man Fetur da ma'adanai, saboda haka gwamnatin tarayya ce ya kamata ta tsara yadda za ta haki wadannan ma'adanai.
Al'umomi a yankin Birnin Gwarin dai sun tabbatarwa da Muryar Amurka cewa banda jami'an tsaron ma, yan bindigan sun kashe masu hakar ma'adanai da kuma 'yan banga a lokacin wannan hari na ranar Litinin ta wannan mako.
Saurari rahoton a sauti: