Taron da ya hada da Sarakuna, malaman addini da kungiyoyi masu zaman kan su da kuma Jam'iyyun siyasa, ya maida hankali ne akan yadda Jam'iyyu za su gudanar da yakin neman zabe da kuma zaben lafiya ba tare da tashin hankali ba.
A hirar shi da Muryar Amurka, Dr. Sale Momale, shugaban hukumar wanzar da zaman lafiyan da ta jagoranci shirya wannan taro. Ya ce sam ba son su ji tashin hankali ko barnan dukiya, dalillan da ya sa ke nan suka gudanar da wannan taro.
Jam'iyyu da dama dai sun halarci wannan taro kuma sun ce matukar za a aiwatar da abubuwan da aka tattauna to za a yi yakin neman zabe da kuma zabe lafiya.
Taron tsara yadda za a yi yakin neman zabe da kuma zaben lafiya dai ya sami halartar manyan sarakunan jahar Kaduna karkashin jagorancin Mai-martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli, da manyan malaman addinin Kirista da Musulmi da kuma kungiyoyin daban-daban a jahar Kaduna.
Saurari rahoton cikin sauti: