Dama dai gwamnatin jahar Kaduna ta taba sa hannu akan dokar dandaka akan masu aikata fyade amma ganin yadda ake samun shakaki game da hukuncin ya sa a jiya Laraba gwamnatin ta kaddamar da rijistar masu fyade don magance matsalar baki daya.
Mataimakiyar gwamnan jahar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe, ita ce ta kaddamar da rijistar a madadin gwamnatin.
Ta ce “Mun lura ne cewa a jihohin da yawa muna samun labarai da ake kawo wa na fyade kuma idan aka yi fyaden, su iyaye ko wadanda aka musu fyaden basu iya zuwa su kai rahoto, wadanda suka samu kai rahoton kuma sai ka ga an addabe su a anguwa ana zagin su.”
Ta kara da cewa, "wannan rajistar da muka kawo idan an samu ya aikata wannan laifi za a saka sunansa a ciki kuma a baza shi a ko ina don kowa ya gane shi."
To ko ta yaya wannan rijistar masu fyade za ta kawo karshen fyaden, mai-baiwa gwamnan jahar Kaduna shawara kan zaman lafiya da daidaita tsakanin al'umomi Rabi Salisu Ibrahim ta dade ta na bincike da bin hakkokin wadanda aka yiwa fyade a Najeriya.
Ta ce, "lallai ana yiwa yara maza kanana kuma ana yiwa yara mata wannan fyade, namiji ta hanyar luwadi, a don haka duk wanda ya aikata wannan danyen aikin asirin shi zai tonu saboda idan aka saka sunansa a cikin wannan rajista ta masu wannan laifi in dai a Najeriya ne ko ya canza jiha ne ya je neman aiki da zarar an buga sunansa cikin rajistan masu fyade a Kaduna sunansa da hotonsa da duk wani bayani game da shi zai fito."
To sai dai duk da kaddamar da wannan rijistar masu fyade, mataimakiyar gwamnan jahar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe ta ce dole sai iyayen yara sun bada gudummawa.
Ga sautin rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna a Najeriya: