KADUNA, NIGERIA - Dama dai ganin yadda adadin yara matan da ake yi wa auren wuri da kuma cin zarafin wasun su, ya sanya kwamishinar mata da walwalar al'umma ta Jihar Kaduna Hajiya Hafsat Mohammed Baba kiran taron musayar ra'ayoyi tsakanin kwamishinonin ma'aikatun mata da kuma ilimi na Jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da nufin nemo mafita kan matsalar baki daya.
Wakilan kwamishinonin ma'aikatun mata daga Jihohin Kano da Zamfara sun ce gwamnati na kokarin magance matsalar auren wuri da cin zarafin yara mata a yankunan su.
Wasu malaman addini ma sun samu halartar wannan taro kuma sun ba da ta su gudummowa.
Taron na yini biyu kan nemo mafita game da matsalar auren wuri da cin zarafin yara mata dai ya tashi a Laraban nan kan cewa wajibi ne kowane ‘dan kasa ya ba da gudummowar magance matsalar baki daya.
Saurari cikakken rahot daga Isah Lawal Ikara: