Duk da fitar da sanarwar tabbatar da harin 'yan-bindiga a yakin Karamar hukumar Zangon Kataf da gwamnatin Jahar Kaduna ta yi, al'ummar yankin ta ce akwai abubuwan da ake boyewa game da harin da su ka yi ikirarin ya kashe sama da mutane 30.
Tsohon Ministan harkokin matasa a Najeriya Barrister Solomon Dalong ya bayyana mahimmancin dake akwai ga al'ummar Najeriya mabiya addinin Kirista da Musulunci su zauna lafiya da juna.
Shirin Manuniya na wannan makon ya maida hankali ne akan Zaben gwamnoni da aka gama a Najeriya da kuma dalilan zuwa kotu da 'yan-siyasa kan yi idan suna zargin murdiya.
An fara kirga kuri'a a wasu rumfunan zabe na kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna saboda yadda aka fara zaben gwamnoni da 'yan majalissa akan lokaci a mafi yawancin rumfunan zabe.
Ganin yadda 'yan siyasa su ka gudanar da yakin neman zabe da kuma sanya addini da malamai su ka yi, ya sa hukumar wanzar da zaman lafiya ta jihar Kaduna kiran wani taron gaggawa, inda ta ja hankalin al'uma da su guji ta da hankali a lokaci da bayan zaben gwamnoni.
Wasu 'yan bindiga sun kai wani hari da ake zargin na ramuwar gayya ne a unguwar Wakili da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, inda su ka kashe mutane da kuma barnata dukiya.
Shirin Manuniya na wannan makon ya duba maganar dage zaben gwamnoni da 'yan-majalissa a Najeriya da kuma kalubalen da aka fuskanta a zaben shugaban Kasa.
Bayan kwashe yini uku da fara zaben shugaban Kasa a Najeriya, Babban malamin zabe mai tattara sakamakon zaben shugaban Kasa a jahar Kaduna ya sanar da sakamakon zaben a daren jiya a Kaduna.
Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa'i ya ce ya na sa ran kotun koli za ta yanke hukunci a ranar Laraba mai zuwa game da da maganar canjin takardun kudi.
Tsohuwar jihar Arewa a karkashin Lord Frederick Lugard, ita ce ta koma jihar Arewa ta tsakiya a alif 1967 kafin daga bisani ta zama jihar Kaduna a 1975. A alif 1987 ne kuma aka cire jihar Katsina daga tsohuwar jihar ta Kaduna, wadda a yanzu ke da kananan hukumomi 23.
Kungiyar Masiyawan Najeriya ta ce daya daga cikin matsalolin da ta ke fuskanta ita ce rashin samun hadin kan sauran al'uma da wariya da ake nuna musu.
A yayin da jam'iyyun siyasa ke ci gaba da yakin neman zabe a Najeriya jam'iyyar NNPP ta kaddamar da gangamin yakin neman zabe na Arewa maso yamma, inda dan takarar jam'iyyar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana gamsuwarsa da amfani da na'urorin da za su hana magudin zabe.
Domin Kari