KADUNA, NIGERIA - Malaman addinin Musulunci da na Kiristoci dai sun shiga fagen yada manufofin wadanda su ke so a zaba a zaben gwamna da na 'yan majalisun jiha ta hanyar amfani da wuraren ibadu, abin da ya kara dumama harkar siyasa a jihar Kaduna.
Shugaban hukumar wanzar da zaman lafiya ta jihar Kaduna, Dr. Saleh Momale ya ce hukumar ta sami labarin cewa akwai ma 'yan siyasar da ke son amfani da matasa don tada hankali.
Babban Sakataren kungiyar Kiristoci a jahar Kaduna, Rebaren Caleb Ma'aji ya ce saka siyasar a cikin addini na da hadari matuka.
Malam Ibrahim Kufena wanda yake sakataren kungiyar Jama'atu Nasrul Islam a Kaduna, shi ma ya ce shigar da harkokin siyasa a masallatai ko majami'u kuskure ne.
Salon yakin neman zaben da aka yi tsakanin 'yan takarar gwamnan jihar Kaduna dai ya baiwa wasu tsoro saboda yadda ya yi zafi, duk kuwa da ya ke zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya ya gudana salun-alun ba rikici a jihar ta Kaduna.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara: