Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya ce yadda aka gudanar da zaben akwai armashi, sai dai kuma ya ja hankalin al'umar jihar Kaduna kan cewa ya kamata mutane su girmama juna su kuma girmama ra'ayoyin juna.
Ya kuma yi kira ga duk wanda ya lashe zabe da ya rungumi dayan su hada hannu su yi aiki tare don ci gaban jihar da ma kasa baki daya.
An dai yi zabe ba tare da tangarda ba a mafi akasarin rumfunan zabe a jihar, duk da cewa mutane ba su fito zabe kamar yadda suka fito a zaben shugaban Kasa da na 'yan majalisar dokoki ba, musamman ma dai a wasu rumfuna da ke kwaryar garin Kaduna.
Duk da canja kudin Najeriya da kuma karancin takardun kudi a hannun mutane, an zargi wasu 'yan-siyasa da yin amfani da kudi da kuma abun masarufi don sayen kuru'u, kamar yadda Haruna Usman ya bayyana. Ko da yake wasu masu zaben sun ce ba su ga inda aka raba kudin ba.
Ya zuwa daren Asabar dai an kammala tattara sakamakon zaben a mafi yawancin rumfuna da mazabu kuma ana sa ran zuwa yammacin Lahadi za a iya samun sakamakon zaben a matakin kananan hukumomi.
Saurari rahoton Isah Lawal Ikara: