Mataimakin shugaban Jami'ar tarayya da ke Birnin Kebbi, Parfesa Mohammad Zayyan Umar kenan ke sanar da sakamakon zaben shugaban Kasa daga kananan hukumomi 23 dake jahar Kaduna inda Jam'iyyar PDP ke kan gaba da kuru'u 554,360, APC ce ta biyu da kuru'u 399,293, Jam'iyyar Labour ke biye mata da kuru'u 284,494 ita kuma Jam'iyyar NNPP ta zo ta hudu da kuru'u 92,969.
Dukkanin wakilin manyan Jam'iyyu hudu da su ka fafata a zaben sun amince da sakamakon kuma sun rattaba hannu.
Kwamishinan 'yan-sandan Jahar Kaduna, CP Yakini Ayoku wanda aka fara tattara sakamakon da shi kuma aka kare zuwa cikin dare ya nuna gamsuwa.
Shima malamin zaben, Parfesa Mohammad Zayyan Umar wanda shi zai kai sakamakon zaben Abuja yau Talata ya ce tattara sakamakon ya gudana cikin armashi.
Wannan ne karon farko da Jam'iyyar adawa ta Labour ta ketaro Kaduna ta sami 'yan majalissar kasa biyu sannan kuma ta sami rinjaye a kananan hukumomi 7 kamar dai yadda ita ma Jam'iyyar PDP wannan karon farko da ta lashe zabe a jahar Kaduna tun bayan faduwar ta zabe a shekarar 2015 saboda ta sami galaba a kananan hukumomi 14 cikin 23 kuma ita ce biyu a duk sauran kananan hukumomin da ba ita ta lashe ba.
Saurari rahoton: