A wani mataki na karfafa gwiwar dakarun Najeriya da ke fafatukar kare kasar, an karrama sojojin kasar da su ka kwanta dama yayin aiki ma kasar.
Najeriya na jagorantar cimma wani muradi na kungiyar tarayyar Afirka na samar da wata rundunar sojojin ruwa ta kasa-da-kasa makamanciyar ta yankin tafkin Chadi don aikin samar da tsaro a yankin gabar tekun Guinea.
Hedikwatar rundunar mayakan ruwan Najeriya ta gano masu ma ta sojin gona a matsayin sojojin ruwa
Rundunar sojin ruwan Najeriya za ta kulla yarjejeniyar aiki da wasu kasashen Afirka don kara tunkarar yanayin tsaro a Gabar Tekun Guinea.
Rundunar 'yan sandan yankin babban birnin Tarayyar Najeriya ta ce jami'anta sun kai wani samame a cikin dajin Udulu da ke karamar hukumar Gegu a jihar kogi da ke makwabtaka da dajin Sardauna na jihar Nassarawa da dukkanninsu ke makwabtaka da yankin babban birnin Tarayyar.
Sa dai tambayar da ake yi ita ce, shin tsaron ya samu? wadanda ke yankunan da kalubalen tsaron ke addaba sun yi tsokaci a shirin Tubalin na Tubalin Tsaro.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta sami nasarar cafke kwamishinan hukumar zaben ta kasa INEC na Jihar Adamawa, Hudu Ari, wanda ya yi riga-malam masallaci wajen ayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa tun ba'a kammala tattara sakamakon baki daya ba.
Rundunar Sojin dai ta gudanar da ayyukan raya ilimin ne domin kara kulla alaka da fararen hula.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinta ta samu nasara ainun wajen shawo kan matsalolin tsaro da ake fuskanta a Najeriya.
Rikicin kabilanci ya da ya barke a unguwar Gwarinpa da ke tsakiyar birnin Abuja tsakanin Hausawa da Gwarawa ya yi sandin mutuwar mutum daya.
Yayin da sauran kasashen duniya suka yi nisa da kwashe 'yan kasashensu daga Sudan mai fama da tashin hankali, Najeriya ta ce yau ko gobe za ta fara jigiliar 'yan Najeriya mazauna Sudan wadanda suka fara kokawa da irin tsaka mai wuyar da suke ciki.
An yi tai kai ruwa rana yayin sake zaben na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya ja hankulan al'umar kasar.
Mai sharhi kan al'amuran diflomasiyya, Bashir Danmusa, ya ce wannan bude- baki da Amurkan ta shirya babban abin a yaba ne domin hakan zai kara karfafa alakar zumunci da fahimtar juna.
Matsalar hare-haren 'yan bindiga ta yi kamari a kauyukan da ke kan iyaka a tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar a 'yan shekarun bayan nan.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan Najeriya CSP Muyiwa Adejobi, a cikin wata sanarwar da ya aike wa Muryar Amurka, ya ce an dauki matakin ne biyo bayan samunsu da laifukan da suka saba aiki.
Masana sun ce duk farar hula da aka kama yana taimakawa 'yan taadda - tamkar ya ci amanar kasa ne.
Shelkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta bayyana cewa, bata fuskantar wata barazanar tsaro da zata kai ga kawo sojojin kasashen waje cikin kasar.
Jirgin ruwan na kasar Denmark da ya iso gabar tekun Guinea daga birnin Amsterdam, ya ratsa kasashen Ghana, Togo, Najeriya, Kamaru da Congo, kafin ‘yan ta’addan su yi awon gaba da shi.
Bababban hafsan hafsoshin Najeriya, Janaral Farouk Yahaya ya aike da sakon gargadi mai zafi ga kungiyar tsagerun ‘yan awaren kudu maso gabashin kasar dake neman ballewa daga Tarayyar kasar
Air Commodore Wap Maigida ya rasu ne a gidansa haka bakatatan a daren ranar Lahadi inda rahotanni suka ce yanke jiki ya yi ya fadi.
Domin Kari