Shugaban Najeriya Sanata Bola Ahmed Tinubu, a karon farko, ya gana da manyan hafsoshi da sauran shugabannin hukumomin tsaron kasar a fadar gwamnati ta ASO Rock da ke birnin Abuja a yau Alhamis.
Shugaba Tinubu ya ja kunnen hukumomin tsaron bisa yadda kowa ke yin gaban kansa wajen aikin samar da tsaro, inda yace lalle za a sake fasalin tsarin tsaron kasar.
Da ya ke wa manema labaru karin bayani jim kadan bayan taron, mai bai wa
shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro Manjo Janar Babagana monguno ya ce shugaba Tinubu zai yi garambawul a bangaren tsaron kana za a kuma duba yadda shi ma sha'anin tsaron ruwa ya ke tangal tangal musammam matsalar satar mai, abin da ya ce ba za a lamunta ba.
A cewar Janar Monguno shugaba Tinubu ya ce dole ne hukumomin tsaron
kasar su yi aiki tare bisa tsari sannan ake tuntuba.
Bayan da dai manyan Hafsoshin su ka yi wa shugaban kasar bayanai, shugaban ya ce dole ne kasar ta ci gaba, kuma abin da ya ke bukata kenan, don haka ya nemi hukumomin tsaron da su kara zage damtse kana su rubanya kokari.
Shugaba Tinubu ya ce ya ce ba zai lamunci yadda talakawa za su rasa makama ba a fannin tsaro kuma za a cimma hakan ne ta hanyar aiki tare, don haka dole ne ai aiki kafada da kafada.
Shugaban kasar ya nemi kwamandojin da su fito da sabon tsari ta hanyar tafiya tare da ainihin mayakan da ke a wuraren da ake fafatawar, kana dole ne a samar wa sojojin dukkan kayan aiki da suke bukata a kuma kula da walwalarsu.
A cewar Janar Monguno shugaba Tinubu ya ce dole ne hukumomin tsaron kasar suyi aiki tare bisa tsari sannan ake tuntuba.
abuja, nigeria —