Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kebe Dala Miliyan Ashirin Don Tunkarar Matsalar Yunwa A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Majalisar dinkin duniya
Majalisar dinkin duniya

Jami'in ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniyar ya ce "koda baya ga matsalar yunwar, an kiyasta kimanin yara dubu dari bakwai ka iya fuskantar matsanancin karancin abinci mai gina jiki da ka iya yi wa rayuwarsu barazana.''

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe zunzurutun kudi har dalar Amurka miliyan ashirin kwatankwacin Naira miliyan dubu goma sha uku da miliyan dari biyu don tunkarar kalubalen matsalar abinci da ya kunshi abinci mai gina jiki a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya

Jagoran ayyukan jinkai na majalisar dinkin duniya a Najeriya, Mathias Schmale wanda ke bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya yi gargadin cewa dole tasa aka dau wannan mataki, duba da irin ja'ibar yunwa da za a fuskanta sakamakon rikicin da yaki ci yaki cinyewa a yankin.

Matthias Schmale
Matthias Schmale

Ya ce za a kuma samar da kudaden ne daga asusun ayyukan jinkai na Najeriya da asusun tunkarar bukatu na gaggawa

Ya na mai cewa wannan matsala ta abinci mai gina jiki ga yara a arewa maso gabashin Najerioyar ta ninka irin wadda ta faru bara sau biyu ko kuma ninki hudu na wanda ya faru a bara waccan.

Kawo yanzu kimanin mutane dubu dari biyar ne aka kiyasta za su fuskanci matsananciyar yunwa a jihohi uku na arewa maso gabas din.

XS
SM
MD
LG