Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Sojojin Ruwan Kasashen Dake Gabar Tekun Guinea


Sojojin ruwa
Sojojin ruwa

Najeriya na jagorantar cimma wani muradi na kungiyar tarayyar Afirka na samar da wata rundunar sojojin ruwa ta kasa-da-kasa makamanciyar ta yankin tafkin Chadi don aikin samar da tsaro a yankin gabar tekun Guinea.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai, babban hafsan-hafsoshin sojojin ruwan Najeriya Vice Admiral AZ Gambo, wanda babban hafsan soja mai kula da manufofi da tsare-tsare Rear Admiral SS Garba ya wakilce shi, ya ce kafa wannan runduna cika wani kuduri ne na tarayyar Afirka, inda kasashen yankin tekun Guinea za su yi hadakar sojojin ruwa don tunkarar kalubalen tsaro a gabar tekun Guinea.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin ruwan Najeriyar vice Admiral AZ Gambo
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin ruwan Najeriyar vice Admiral AZ Gambo

Ya kuma ce, ko da yake cikin watanni uku zuwa shida da suka gabata an dan sami akasi a yankin ruwan kasashen Cote d'Voire da Kamaru, babu wani abu irin haka da ya faru a yankin ruwan Najeriya, amma duk da haka suna ganin larurar da ta shafi kasa daya tamkar ta shafesu ne gaba daya, don haka wannan hobbasa lallai zai taimaka wajen samar da tsaro a gabar Tekun Guinea.

Da yake amsa tambayar wakilin Muryar Amurka kan ko wacce kasa ce zata dauki hidimar wannan babban aiki? Babban hafsan ya ce aikin na hadaka ne, inda ko wacce kasa zata sanya kudin karo-karo a asusun kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, ita ma kungiyar zata samar da wasu kayayyaki ga rundunar.

Sai dai ko wacce kasa da jirgin yakinta za ta je kuma ita zata kula da shi.

Jirgin ruwan sojojin Najeriya (Facebook/ Nigerian Navy)
Jirgin ruwan sojojin Najeriya (Facebook/ Nigerian Navy)

Farfesa Mohammed Tukur Baba da ke sharhi kan sha'anin tsaro, ya ce rundunar sojan ruwan ta kasa-da-kasa lallai zata yi tasiri sosai, duba da irin kalubalen tsaro kamar fashin teku, safarar miyagun kwayoyi, da sauran ayyukan ta'addanci da ake yi a kan ruwa.

Farfesa Mohammed ya kara da cewa idan aka yi la'akari da yankin ruwa kama daga Afirka ta Yamma har zuwa yankin Afirka ta tsakiya, wurare ne da ake fama da matsalar tsaro, a saboda haka kafa wannan rundunar hadin gwiwa ka iya yin tasiri wajen daidaita al'amura.

Saurari rahoton cikin sauti:

Za a Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Sojojin Ruwan Kasashen Dake Gabar Tekun Guinea
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

XS
SM
MD
LG