Amurka ta yi matukar damuwa da tashe-tashen hankula, da munanan hare-hare a kan fararen hular Sudan da kungiyar ‘yan tawayen RSF da rundunar sojin kasar ke kaiwa, a cewar jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield:
Hare-haren da sojin Isra’ila suka kai a fadin zirin gaza sun hallaka Falasdinawa 20 a yau Litinin, ciki harda wasu mutum 6 dake zaune a tantunan da ‘yan gudun hijira ke samun mafaka, a cewar jami’an bada agaji
Gwamnatin Biden ta sahalewa Ukraine yin amfani da makaman da aka kera a Amurka wajen kai hare-hare cikin Rasha, kamar yadda wasu jami’an Amurka 2 da wata majiya dake da masaniya game da shawarar suka bayyana a jiya Lahadi
Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce a ranar Alhamis ya kara yawan man da ake hakowa zuwa ganga miliyan 1.8 a kowace rana tare da yiyuwar adadin ya kai miliyan biyu a karshen shekara
Kamfanin Dillancin Labaran kasar Syria SANA ya ruwaito cewa, ya jiyo daga majiyar sojan kasar cewa mutaum 15 sun mutu yayin da 16 suka jikkata, sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan wasu gine-ginen gidaje da ke wajen birnin Damascus na kasar Syria a ranar Alhamis
Yawaitar hauhawar farashi da tashe-tashen hankulan ‘yan tada kayar baya sun sanya da kyar ‘yan Najeriya mazauna jihar Borno dake yankin Arewa maso gabashin kasar ke iya ci da iyalansu
Ana sa ran zabebban shugaban Amurka Donald Trump ya dauki dimbin matakan zartarwa a ranarsa ta farko a fadar white house domin tsaurara dokokin shige da fice tare da rushe babban shirin Joe Biden na shiga kasar ta hanyar doka, kamar yadda wasu majiyoyi 3 da suka fahimci batun suka shaidawa Reuters
Domin Kari