JOS, NIGERIA —
A shirin Zamantakewa na wannan makon mun sauka ne a masarautar jihar Neja a Najeriya, inda masarautar ta kabilar Gbagi ta baiwa wasu Fulani sarauta don kara dankon zumunci da samar da zaman lafiya tsakanin kabilun biyu.
Jihar Neja kamar wasssu jihohin Najeriya na fama da matsalolin tsaro, ciki har da rikicin makiyaya da manoma, matakin da masarautar ta Minna ta dauka na nada wadansu Fulani a matsayin wakilai, da yakinin zai saukaka tashin hankalin.
Saurari cikakken shirin da Zainab Babaji ta gabatar:
Dandalin Mu Tattauna