ABUJA, NIGERIA —
A shirin Lafiya na wannan makon mun yi duba kan ranar wayar da kai game da cutar daji, inda muka tattauna da kwararru kan maganin cutar daji, da wasu daga cikin kungiyoyin kula da masu fama da cutar da kuma wadanda suka yi fama da cutar.
Hukumar lafiya ta duniya ta ware ranar 4 ga watan Febrairu na kowace shekara a matsayin ranar yaki da cutar daji ta duniya wanda ya samo asali sakamakon yarjejeniyar samar da bakin zare don yaki da cutar daji wanda aka sanya wa hannun a kasar Paris shekaru 25 da suka gabata.
Saurari cikakken shirin da Hauwa Umar ta gabatar:
Dandalin Mu Tattauna