Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SHARHIN AMURKA: Ranar Shugaban Kasa Ta Bana (2025)


President's Day
President's Day

Litinin ta 3 a watan Febrairu ce ranar shugaban kasa a Amurka. Tunda fari an ware ranar ce da nufin taya George Washinton murna, shugaban kasar na farko, tun daga 1968 ranar hutun ta girmama Abraham Lincoln shima. A yau ranar ta kasance ta tunawa da dukkanin shugabannin da suka mulki kasar

An fara bikin ne a matsayin tunawa da zagayowar ranar haihuwar george washington ta 22 ga watan febrairu. Fiye da duk wani daya rayu a zamaninsa, Washington ya zama jagora ga makomar Amurka ta hanyar yakin juyin juya halin da abinda ya biyo bayansa, rikicin shekaru 6 da ya kawo karshen mulkin mallakar da kasar ta fara tafiya akai tare da kafa nata sabon tafarkin mulkin dimokiradiya mai tsarin wakilai.

Tabbas, ana yawan kiran Washington da uban kasar, ba wai kawai saboda nasararsa a matsayin kwamandan soja ba. Hakika, ya kafa misalai ga dukkanin masu bibiyar rayuwarsa ta farar hula bayan yaki a lokacin da ya shugabanci kasar.

Ya dora kasar a kan nagartaccen tafarkin dogaro da kai a fannin samun kudade tare da yin bikin matashiyar kasar a lokacin ciwon nakudar da cikin sauri ya haifar da daidaitacciya kuma halastacciyar gwamnatin dimokiradiya.

Sakamakon sauka da yayi bisa radin kansa bayan shafe wa'adi 2 na shekaru hurhudu, da kuma tabbatar da musayar mulki cikin lumana ga shugaban da aka zaba ya gaje shi, George Washington ya kafa wani misali mai muhimmanci ga dukkanin shugabanin da zasu zo nan gaba.

Idan da ba don irin jagorancin Washington ba, da akwai yiyuwar Amurka ba za tayi irin bunkasar data yi ba a yau. Haka kuma, Abraham Lincoln wanda ranar haihuwarsa ta kasance 12 ga watan Fabrairu, ya kada Amurka daga dulmiya a yakin basasar da ka iya janyo rabewarta.

Gabanin yakin basasar, Amurka ta kasance wani dandazon manyan kungiyoyin siyasa a karkashin gwamnatin tsakiya mai rauni, yanzu ga kasar da ta farfado daga kazamin yakin basasar shekaru 4 na tsaye a karkashin babbar gwamnati kakkarfa.

Sai dai kwarewar Lincoln wajen iya dunkule ra'ayin al'ummar jihohin arewacin kasar da kuma yadda tattaro daidaito ra'ayin siyasa akan bukatar haramta bautar da dan adam ya sabbaba samun galaba akan jihohin da ke neman ballewa sannan daga bisani ya hade kasar sabanin yadda take a baya.

George Washington da Abraham Lincoln shugabanin ne na lokacin yaki wadanda suka fahimci bukatar hade kan al'umma karkashin gwamnati mai karfe.

Amurka na alfahari da samun zaratan shugabani-a zahirin gaskiya kadan daga cikinsu sun yi abin a yaba-amma babu wadanda tasirinsu ya kai na George Washington da Abraham Lincoln.

A yau muna murnar tunawa dasu tare da karrama wadanda suka dabbaka gadon da suka bari tsawon lokaci.

Wannan sharhi ne da ke nuna manufofin Amurka da cibiyoyinta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG