Uganda ta tabbatar da barkewar annobar Ebola a Kampala, babban birnin kasar, inda mutumin farko da aka tabbatar yana dauke da cutar ya mutu a jiya Laraba, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta bayyana a yau Alhamis
A yau Laraba ne wani karamin jirgin sama dauke da ma’aikatan hakar mai a jihar Unity ta Sudan ta Kudu yayi hatsari tare da hallaka mutane 20, a cewar hukumomi
Turmutsutsin da ya afku da goshin asubahi a bikin bautar kogin maha Kumbh Mela mai tsarki dake arewacin indiya ya hallaka gomman mutane a yau Laraba
A yau Talata MDD tace akwai matukar damuwa dangane da yanayin bada agaji a garin Goma na Jamhuriyar Congo da aka yiwa kawanya, ganin yawan mutanen da aka raba da muhallansu, ga karancin abinci da satar kayan agaji da ambaliya ga asibitoci na marasa lafiya da kuma yadda fyade ya zama ruwan dare
Batun aure tsakanin masu jinsi iri daya, kawo karshen ba da shaidar kasa ga jariran da iyayensu ba ‘yan kasa ba, da kuma tasa keyar bakin haure fita daga Amurka ya janyo ce-ce-ku-ce daga kungiyoyi da yarjejeniyoyi na kasa da kasa, wasu rahotanni
Domin Kari