ABUJA, NIGERIA —
A shirin Tubali na wanan makon wata kungiyar kasa da kasa da take tattauna matsalolin tsaro da bayanan sirri wacce ke aiki da kwamitocin tsaro na majalisun kasashen duniya ta nada wani ‘dan Najeriya a matsayin daraktanta, kuma ‘dan kwamitin amintattu.
Wannan nadin na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma jagoran kwamitin tsaro na majalisar dokoin Amurka, Congressman Robert Pittengen ya sanyawa hannu.
A hirarsa da Muryar Amurka Shaban Sharada ya yi bayanin irin rawar da zai taka da kuma irin alfanun da Najeriya zata cimma a dalilin hakan.
Saurari cikakken shirin da Hassan Maina Kaina ya gabatar:
Dandalin Mu Tattauna