Ghana, kamar yawancin kasashen Afrika rainon Ingila, ta na zaben Shugaban kasa da ‘yana Majalisa a duk shekaru hudu domin su yi wa kasa aiki. Shugabannin kasa na da wa’adi biyu ne kawai da su ke iya zama a mulki amma su ‘yan Majalisa su nada hurumin zarce hakan.
Masu fashin baki su kan takaita tarihin zaben Ghana zuwa daga jamhuriya ta hudu da ta fara aiki a shekarar 1992 bayan kasar ta amince ta koma mulkin farar hula a zamanin mulkin soja karkashi jagorancin JJ Rawlings.
Karo na takwas kenan da Ghana zata yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a yau Litimin bakwai ga watan Disamban shekarar 2020, inda za a fafata tsakanin ‘yan takara 12, ciki har da shugaban kasa Nana Addo Dankwa Akufo Addo na jami’iyar NPP mai mulki da John Dramani Mahama tsohon Shugaban Kasa na babbar jami’iyyar adawa ta NDC.
Ghana, kamar sauran kasashen Afrika ta kan fuskancin yakin neman zabe mai ciki da fargaba saboda kalamai masu gauni da ‘yan siyasa ke fada wa juna kamar yanda aka gani a gangamin wannan shekara, lamarin da kan kai ga samun ‘yan rikice rikice.
Muhimman matakai da hukumomi ke dauka, kama daga hukumomin tsaro, hukumar zabe, hukumar da wayar da kan jama’a kungiyoyin jama’a da kungiyoyi masu zaman kansu na bada gudunmuwa wurin samun zabe cikin kwanciyar hankali.
Duk da cewar a kan samu rashin fahimta game da sakamakon zabe, toh amma galibi ana shawartar masu takara da su nemi hakkinsu a kotu a maimakon su tada fitina a cikin kasar.
Saurari cikakken rahoton Baba Yakubu Makeri ciki sauti: