Da ya ke Magana a lokacin da ya ke tare da shugaban jam’iyyar ANC mai mulki ta Afrika ta kudu kuma Ministan albarkatun kasa da makamashi na Afrika ta kudu, Gwede Mantashe, wanda ya kai ziyara birnin tarayya Abuja ranar Juma’a 4 ga watan Disamba a matsayin wakilin kasarsa na musamman, shugaba Buhari ya ambaci ziyarar da ya kai Afrika ta kudu ta baya-baya, lokacin da shi da shugaba Cyril Ramaphosa su ka tattauna akan warware rikicin baki tsakanin kasashen biyu.
“Akwai ‘yar matsala tsakanin kasashenmu. Na je Afrika ta kudu kuma mun tattauna kan warwarre matsalar, abinda shugaban Najeriya ya fada wa wakilin kenan.
Shugaban ya umurci Ministan man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya yi aiki da takwaran aikinsa na Afrika ta kudu don ya dawo mashi da bayani.
Ministan na Afrika ta kudu, wanda ya kai sakon wasika daga shugaba Ramaphosa, ya ce dagantakar da ke tsakanin Najeriya da kasarsa na da muhimmanci wajen bunkasa nahiyar Afrika.
Yayin da ya jaddada cewa ya kamata kasashen biyu su yi aiki a matsayin kawaye, Mantashe ya ce dagantakar ce za ta tantance makomar Afrika.