Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kwace Wani Yankin Dake Hannun 'Yan Bindigan Tigray


Firai Ministan Sudan
Firai Ministan Sudan

Ma’aikatar sojin Sudan na ci gaba da jibge dakarunta a yankin noman kasar da ake takaddama akai da yankin Tigray na makwabciya kasar Habasha da yaki ya daidaita. Sai dai gwamnatin Sudan taki cewa uffan a kan jibge sojojin.

Sojojin Sudan sun koma kan filayen noman dake kan iyaka da Habasha a ranar Alhamis kana suka baza kan su a kan yankin kasar da ‘yan bindigan Habashan suka kwashe sama da shekaru 25 suna rike da iko wurin, a wani dadadden rikici tsakanin Khartoum da Addis Ababa.

Kungiyar ta ‘yan bindigan Habasha suna kiran yankin Shefta mai yawan harkoki a lokacin rani na kowace shekara, suna satan amfanin gona a Fashaqa da wasu unguwanni da Sudan take da’awar nata ne.

Wani jami’in tsaron yankin da ya nemi a sakaya sunan sa, ya fadawa Muryar Amurka cewa sojojin Sudan sun kwace ikon yankin.

Sudan tana daukar nauyin ‘yan gudun hijiran Habasha da suka arce daga yakin Tigray da ya barke a cikin watan Nuwamba tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ‘yan bindigan Tigray ta Tigray People’s Liberation Front (TPLF), a takaice.

Sama da ‘yan gudun hijira dubu 43 ne aka karkasa su zuwa sansanoni a biranen Sudan guda biyu da suka hada da Qadarif da Kassala.

Hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta ‘yan gudun hijiran zasu kai dabu dari nan da ‘yan makwanni masu zuwa.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG