Shugaban kwamitin majalisar nakasassu a Ghana, Yaw Ofori Debra ya yi kira ga hukumar zaben kasar da ta tabbatar da cewa an ba membobin kungiyarsa goyon baya da kulawa a rumfunan zabe, ya na mai cewa yawancin nakasassu su na bukatar a bi su a hankali don ba su damar sauke hakkinsu na dimokradiyya.
Mr. Debra ya fadi cewa tattaunawar da suka yi da hukumar zaben ta haifar da kyakkawan sakamako kuma sun gamsu da shirye-shiryen zaben don tabbatar da cewa nakassasu sun samu kulawar da ta dace a lokacin kada kuri’unsu a lokacin zaben.
Ya kara da cewa akwai nakasassu da dama a Ghana kuma dukkansu su na bukatar damar kada kuri’unsu cikin kwanciyar hankali.
Mr. Debra ya yi kira ga al’ummar kasar Ghana da su gudanar da zabe cikin nasara da kwanciyar hankali ba tare da kowanne irin tashin hankali ba, kamar yadda dimokradiyya ta bai wa kowanne dan kasa dama ya kada kuri’arsa, kuma ya zabi abinda ya ke so.
Ga cikakken rahoton Ridwan Abbas daga Ghana: