Ranar 20 ga wannan watan za'a gudanar da zaben shugaban kasar Nijar zagaye na biyu amma mahukuntar kasar sun zargi 'yan adawa da yin farfaganda a wuraren da suke da karfi suna yiwa dan takararsu kemfen.
Inji mahukuntan kasar 'yan adawa na bin dare suna fadawa mutane su zabi Hamma Ahmadou.
To saidai kakakin jam'iyyar PNDS mai mulki reshen Kwanni yace janyewar 'yan adawan yaudara ce domin har gobe basu bar yin kemfen ba musamman inda suke ganin suna da karfi. Jam'iyyar PNDS tace su yaki zasu shiga na neman zabe babu ja da baya.
'Yan adawa sun yi fatali da zargin suna cewa masu mulki ne suka sauya salon yakin neman zabe suna bin dare suna kemfen inji Alhaji Isa Marai kakakin jam'iyyar MODEN Lumana.
Ga karin bayani