Wa'adin shekaru biyar na 'yan majalisun dokokin kasar Nijar ya cika jiya da misalin karfe 12 na dare kenan ikon yin dokoki da suke dashi shekaru biyar da suka gabata ya zo karshe yau da safe.
Jama'ar kasar suna cigaba da yin furuci game da karshen wa'adin lokacin majalisun. Bangaren masu mulki wato jam'iyyar PNDS ana ta yabo da guda game da ayyukan da 'yan majalisun suka yi cikin shekaru biyar.
Alhaji Mani na jam'iyyar PNDS Yace sun godewa Allah saboda idan sun kawo wani kuduri na cigaban kasa 'yan adawa sukan taru su amince da kudurin ya zama doka. Misali lokacin da kasar zata aika da sojojinta kasar Mali 'yan adawa sun amince ba tare da wata hamayya ba.
Amma kuma a bangaren 'yan adawa Alhaji Abdulmummuni na jam'iyyar MNSD Hankuri yana cewa a jamhuriyar Nijar 'yan majalisar dokokin sun zama 'yan amshin shatan gwamnati. Ba kasa suka yiwa aiki ba jam'iyyunsu suka yiwa aiki. Kowane dan majalisa umurnin jam'iyyarsa yake bi. Dan majalisar kasa nauyin kasa ke kansa ba na jam'iyya ba.
Ga karin bayani.