Ma’aikatar tsaron kasar ce ta fitar da wata sanarwa ta kafar talbijin, inda Kanar Ledru Moustapha ya bayyana cewa wasu mahara akan babura hudu da wata mota kirar Toyota suka kai harin.
A wani hari na daban, wasu dakarun kasar ta Nijar sun samu raunuka yayin da wasu masu harin kunar bakin wake su biyar suka mutu a wani harin kwantan-bauna da aka kai a yankin Diffa, harin da hukumomin kasar suka dora alhakinsa akan mayakan Boko Haram.
Wadannan hare-hare- na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Nijar ke shirin yin zaben shugaban kasa a zagaye na biyu.
Wani kakakin bangaren ‘yan adawa, Amadou Bjibo, ya yi kira ga masu kada kuri’a da su kauracewa zaben, domin a cewarsa zaben da aka yi ranar 21 ga watan Farbrairu yana cike da kura-kurai.