Hukumar zabe ta jamhuriyar Nijar CENI, ta tabbatar da cewa ta kammala dukkan shirye shirye domin gudanar zaben fidda gwamnai da za'a yi Lahadi,20 ga watan Maris.
Zaben da za'a yi tsakanin shugaban kasa mai ci ne Muhammadu Isouffe, da kuma madugun 'yan hamayya,kuma tsohon kakakin majalisa Hamma Amadou, wanda ahalin yanzu aka kai shi kasashen wajen domin jinya. Kamin haka dai Hamma yana gidan kaso, inda hukumomin kasar suka tsare shi kan zargin fasakorin jarirai.
Amma 'yan hamayya suna kan bakarsu na ci gaba da kiran magoya bayansu su kauracewa wannan zabe, domin suna zargin an tafka magudi tun a zagaye na farko, kuma ba'a yi musu adalci ba da suka daukaka kara zuwa kotun tsarin mulkin kasar.
Haka nan sun kawo batun ci gaba da tsare dan takararsu Hamma Amadou.
Ibrahim Ka'almaseeh Garba ya aiko da wannan rahoto.