Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Umarci Baitul Malin Amurka Ta Daina Kera Sabbin Kwandaloli

 Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump
Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump

Trump ya maida batun zaftare kasafin kudin gwamnatin tarayyar Amurka wani babban jigo na gwamnatinsa, inda aka dorawa tawagar DOGE karkashin jagorancin attajiri Elonk Musk alhakin bankado yadda ake kashe kudaden gwamnati.

A jiya Lahadi, Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa baitul malin kasar data dakatar da samar da kudaden kwandala, inda ya gabatar da hakan a matsayin wani yunkuri na rage kashe kudin gwamnati.

“Amurka ta jima tana kera kudade kwandala wanda a zahiri ake kashe fiye da senti 2 akan yin hakan. Wannan babbar asara ce!” kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social Platform.

“Na umarce sakataren baitul malinmu ya dakatar da kera sabbin kwandaloli. Bari mu yage wannan barnar daga cikin kasafin kudin kasarmu, koda kuwa sisi-sisi zamu rika ragewa a lokaci guda,” kamar yadda ya kara bayyanawa.

Akwai yiyuwar sai umarnin na Trump ya bukaci amincewar ‘yan majalisa saidai sakataren baitul malin Scott Bessent na iya dakatar da kera sabbin kwandalolin ne kawai, kamar yadda farfesan tsimi da tanadi Robert Triest na jamai’ar Northeastern ya wallafa a watan Janairun daya gabata.

Trump ya maida batun zaftare kasafin kudin gwamnatin tarayyar Amurka wani babban jigo na gwamnatinsa, inda aka dorawa tawagar DOGE karkashin jagorancin attajiri Elonk Musk alhakin bankado yadda ake kashe kudaden gwamnati.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG