Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Bai Kara Haraji Nan Take Ba Kamar Yadda Ya Alkawarta


Shugaban bai maka harajoji nan take ba kamar yadda ya alkawarta, saidai ya umarci hukumomin gwamnati da su yi “bincike tare da gyarar da ta dace” a bangaren kasuwancin Amurka da ya dade yana fuskantar koma baya da rashin adalci da suka shafi karya darajar kudinta da wasu kasashe ke yi.

Shugaban Amurka Donald Trump wanda aka rantsar a matsayin shugaban Amurka a jiya Litinin, ya fada cikin jawabin shi na kama aiki, cewa, Amurka zata samu kudaden shiga masu yawa da za ta samu ta hanyar sanya haraji a kudaden kayan da ake shigo da su kasar, yayin da gwamnatin shi zata yi kokari ta farfado da kamfanonin Amurka.

“Haraji zai azurta Amurka sosai,” abin da Trump ya fada ma magoya bayan shi a dandalin Capital One Arena a Washington DC kenan. Ya kara da cewa, “Zai taimaka ya farfado da kasuwancin Amurka da ya samu koma baya.”

Jinkirin da yayi a ranar farko da ya kama aiki, alama ce dake nuna cewa zai yi nazari a game da batun sanya haraji, batun da ya sa mahukunta da masu zuba jari suka firgita, kuma yanzu ya sa aka samu sauki a fannin hannayen jari a fadin duniya da kudaden wasu manyan kasashe dake gogayya da dalar Amurka.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG