Kungiyar ta Amnesty, wacce ke adawa da akidar hukuncin kisa a duk duniya, ta ce kasashen China, Belarus da Vietnam ne suka fi duk sauran kasashe rufe asirin yawan mutanen da suke hallakawa a hukumance, abinda suke dauka a matsayin “asirin kasa” ne.
Kiddidigar da Amnesty ta gabatar kan hukuncin kisan da aka aiwatar a kasashe 23 na duniya a shekarar 2016, ta nuna cewa mutanen 567 Iran ta kashe a bara, abinda ya sa kasar ta zo ta biyu bayan China.
Saudi Arabia ce kuma ta zo ta uku da mutane 154, sai Iraq mai 88 da kuma Pakistan inda aka kashe mutane 87.
Duka-duka a duniya mutane 1,032 hukumomi suka kashe a kasashen duniya a shekarar ta 2016.
Facebook Forum