Da yake zantawa da manema labarai jiya a birnin Moscow, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron ta Rasha, Lieutenant General Sergei Rudskoi yace rundunar mayakan Rasha da Syria zasu saurara da fadan daga tsakanin karfe takwas na safe zuwa karfe hudu na rana a ranar 20 ga wannan watan Oktoba a yankin Aleppo don bada daman fidda fararen hula da masu ciwo da wadanda suka samu rauni daga yankin.
Rudskoi yace akwai tituna biyu da za ayi amfani dasu wurin fita daga birnin.
Sai dai duk da hakan, Amurka da wasu kasashen Turai suna zargin Rasha da Syria da aikata kisan kiyashi, amma jami’an Rasha sun musunta wannan zargin.
Mayakan Rasha da na Syria sun share makkoni suna ta sakin ruwan bama baman a kan bangaren da yan tawaye suke a birnin Aleppo, a daidai lokacinda shugaban Syria Basah al-Assad ke kokarin kwace ikon birnin da a can da yake cike da hidimomin kai da kawon jama’a kafin jama’a su fara yi wa gwamnati bore a cikinsa kamar shekaru shidda da suka shige.