Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Yarda Yana Hasarar Goyon Bayan Mata


Donald Trump dan jam'iyyar Republican dake neman shugabancin Amurka
Donald Trump dan jam'iyyar Republican dake neman shugabancin Amurka

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump ya yarda cewa yana samun rashin goyon bayan mata, amma ya dora laifin akan kafofin yada labarai da suka rawaito mata da yake ikirarin sunyi masa kage kan neman lalata dasu.

Trump ya rubuta a shafinsa na tweeter cewa alkaluman takara dake tsakanin sa da Yar takarar Democrats Hillary Clinton sun nuna cewa tazararsu kadan ce “Ku duba yadda na rasa lambobi masu yawa daga masu zabe mata saboda labaran shaci fadi da basu taba faruwa ba. Kafofin yada labarai na magudin Zabe.

Ya maimaita cewa Kafofin yada labarai na nuna son rai akansa “ Sakamakon kokarin hadin kai da Kamfe na Clinton, suka saka abubuwan da basu taba faruwa ba a labarai.

Mai yi ma Clinton takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Tim kaine daga Jihar Virginia, yayi shagube game da wadannan zarge-zargen da Trump yake yi, yana mai fadawa wani dan jarida cewa Trump yana dora laifi kan kafofin yada labarai. Yana dora laifi kan 'yan jam'iyyarsa ta Republican. Yana fadin cewa Amurka ba zata iya gudanar da zabe tsakani da Allah babu ha'inci ba. Kai, duk abinda ya shiga cikin kwakwalwarsa haka yake yankowa ya fada a saboda ya san cewa zai sha kaye."

Adadin kuri'un neman ra'ayoyin jama'a na kasa da kungiyar Real Clear Politics ta harhada ya nuna cewa Clinton tana gaban Trump da maki biyar da rabi. A jiya lahadi an fito da wasu muhimman kuri'un nneman ra'ayoyin jama'a guda biyu, inda ta Washington Post da ABC News ta nuna cewa Clinton tana gaba da maki hudu, yayin da ta NBC News da Wall Street Journal ta nuna cewar Clinton ta ba Trump ratar maki 11 ne a tsakanin masu jefa kuri'a na kasa.

XS
SM
MD
LG