Shugaban Kurdawa Masoud Barzani a wani taron yan jarida da aka nuna a tashoshin telbijin a jiya Litinin yace an yi nasarar akalla kilomitoci 200 a cikin kwana daya kacal da fara wannan barin wuta.
Wannan dai shine farmakin sojin mafi girma tun bayan da rundunar Amurka ta fice daga kasar shekaru biyar da suke wuce, sai dai wannan hare haren na janyo fargaba a kan lafiyar dubban fararen hula dake zaune a yankin.
Wannan yunkurin sojin na ‘yanta birnin Mosul daga IS na hadin-gwiwa ne da ya hada hancin rundunonin sojan Kurdawa da yan sandan tarayya da mafarautan Sunni da kuma mayakan yan Shi’a. Rundunar hadin guiwa karkashin jagorancin Amurka da suka share tsawon shekaru biyu suna fatatakar mayakan ISISI daga sama a Iraqi da Syria su ma suna cikin wannan fafatikar da ake ta ‘yanttarda birnin na Mosul.